‘Yan bindiga sun kakaba harajin naira miliyan 5 a wasu kauyukan Katsina

0
‘Yan bindiga sun kakaba harajin naira miliyan 5 a wasu kauyukan Katsina

‘Yan bindiga sun kakaba harajin naira miliyan 5 a wasu kauyukan Katsina

Spread the love

‘Yan bindiga sun kakaba wa wasu al’ummomi harajin naira miliyan biyar a ƙananan hukumomin Danmusa da Matazu da ke Jihar Katsina, lamarin da ya jefa mazauna yankunan cikin tsananin fargaba.

Rahotanni sun nuna cewa kauyukan da abin ya fi shafa sun hada da Mara Dangeza, Unguwar Tofa da kuma Gidan Goge, inda aka bai wa mazauna wa’adin biyan kudin tare da barazanar kai hari idan suka ki.

Saboda tsoron hare-hare da rashin ikon biyan kudin, wasu daga cikin mazauna kauyukan sun fara barin gidajensu domin neman mafaka a wurare masu aminci.

Ana ganin wannan mataki a matsayin wata sabuwar dabara da ‘yan bindiga ke amfani da ita wajen karbar kudade daga al’ummomin karkara a yankin Arewa maso Yamma.

Al’ummomin da abin ya shafa sun yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su gaggauta daukar mataki domin dakile matsalar da kuma kare rayuka da dukiyoyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *