‘Yan sanda sun cafke mutane shida bayan rikicin daba a Kano

0
Yan sanda sun kama mutane shida a rikice-rikicen daba a Kano

Yan sanda sun kama mutane shida a rikice-rikicen daba a Kano

Spread the love

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kano ta samu nasarar dakile wani mummunan rikici da ya barke tsakanin kungiyoyin daba a unguwar Gyadi-Gyadi, inda ta kama mutane shida da ake zargi da hannu a lamarin.

Lamarin ya faru ne bayan da ‘yan sanda suka samu kiran gaggawa cewa wasu ‘yan daba sun shirya fada, wanda hakan ya sa jami’an tsaro suka gaggauta zuwa wurin domin hana rikicin yaduwa.

A cewar kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar, CSP Abdullahi Kiyawa, saurin daukar matakin da jami’an suka yi ya taimaka wajen dawo da zaman lafiya tare da hana barkewar rikici mai tsanani a yankin.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya faru ne da misalin karfe 1:20 na rana, inda ake zargin kungiyoyin ‘yan daba masu gaba da juna ne suka yi yunkurin arangama kafin jami’an tsaro su shawo kan lamarin.

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike kan lamarin, tare da daukar matakan shari’a a kan wadanda aka kama domin tabbatar da doka da oda a jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *