Shugaban Bangladesh Mohammed Shahabuddin ya yi murabus saboda rashin lafiya
Shugaban Bangladesh Mohammed Shahabuddin ya yi murabus saboda rashin lafiya
Shugaban ƙasar Bangladesh, Mohammed Shahabuddin, ya yi murabus daga mukaminsa shekaru biyu kafin karewar wa’adinsa na shekaru biyar.
Shahabuddin mai shekaru 76 ya bayyana cewa matsananciyar rashin lafiya ce ta tilasta masa barin kujerar shugaban ƙasa.
A cikin sanarwar da aka fitar, Shahabuddin ya ce likitoci sun gano yana fama da cutar Autonomic Neuropathy, wadda ke sa ya kan rasa hayyacinsa na ɗan lokaci, lamarin da ya ce ya hana shi ci gaba da gudanar da nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora masa.
Murabus ɗin ya zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar matsin lamba daga jam’iyyun adawa da kuma sauye-sauyen siyasa da suka biyo bayan hambarar da tsohuwar Firaminista Sheikh Hasina a shekarar 2024.
Bayan murabus ɗin, kakakin majalisar dokokin Bangladesh ne zai riƙa gudanar da ayyukan shugaban ƙasa na riƙo har sai an zaɓi sabon shugaban ƙasa cikin kwanaki 90, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.
