Tambuwal ya janye daga takarar sanatan Sokoto ta Kudu
Sanata Aminu Tambuwal
Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma sanata mai wakiltar Sokoto ta Kudu, Aminu Waziri Tambuwal, ya sanar da janyewarsa daga takarar kujerar Sanatan Sokoto ta Kudu gabanin zaɓen shekarar 2027. Rahotanni sun bayyana cewa matakin ya zo ne bayan tattaunawa da manyan jiga-jigan siyasa a jihar.
An ruwaito cewa Tambuwal ya yanke shawarar ne domin bai wa wani tsohon kwamishina damar tsayawa takarar kujerar, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin magoya bayan jam’iyyar PDP da sauran masu ruwa da tsaki a siyasar jihar Sokoto.
Wasu daga cikin magoya bayan tsohon gwamnan sun bayyana matakin a matsayin siyasa mai nuna sadaukarwa da kishin jam’iyya, inda suka ce Tambuwal ya sake nuna cewa yana fifita haɗin kai da ci gaban siyasa fiye da muradin kansa.
Sai dai wasu masu sharhi kan harkokin siyasa sun bayyana cewa janyewar tasa na iya sauya yanayin siyasar Sokoto ta Kudu, musamman ganin irin tasirin da Tambuwal ke da shi a jihar da kuma a matakin ƙasa baki ɗaya.
Har zuwa yanzu, Tambuwal bai fito fili ya bayyana cikakken dalilin janyewar tasa ba, amma ana ganin matakin zai iya haifar da sababbin sauye-sauye a fafatawar siyasar 2027 a jihar Sokoto da Najeriya baki ɗaya.
