Atiku ya mayar da takardun tsayawa takara a ADC
Atiku ya mayar da takardun tsayawa takara a ADC
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya miƙa takardun neman takarar sugaban ƙasa a jam’iyyar African Democratic Congress domin zaɓen shekarar 2027.
Atiku ya gabatar da takardun ne a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja tare da bayyana cewa lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su haɗa kai domin ceto ƙasar daga matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro.
A jawabin da ya yi yayin miƙa takardun, Atiku ya roƙi ‘yan Najeriya musamman matasa da masu kishin ƙasa da su shiga tafiyarsa domin samar da sabuwar Najeriya mai ci gaba.
Ya ce ƙasar na buƙatar shugabanci nagari wanda zai mayar da hankali wajen bunƙasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma inganta rayuwar jama’a.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa jam’iyyar ADC ta zama mafakar sabbin sauye-sauye a siyasar Najeriya, yana mai cewa mutane da dama daga jam’iyyu daban-daban na ci gaba da shiga cikinta saboda burin ganin an kawo canji a shekarar 2027.
Rahotanni sun nuna cewa Atiku ya biya kuɗin fom ɗin takarar shugaban ƙasa har Naira miliyan 90 kafin miƙa takardun nasa.
Matakin nasa ya ƙara nuna cewa tuni ya fara shirye-shiryen neman shugabancin ƙasa a karo na gaba bayan ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa ADC a shekarar 2025.
Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa matakin Atiku zai ƙara zafafa siyasar Najeriya yayin da jam’iyyun adawa ke ƙoƙarin haɗa kai domin kalubalantar jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
Ana sa ran fitattun ‘yan siyasa da magoya baya za su ci gaba da bayyana matsayinsu game da takarar Atiku a cikin kwanaki masu zuwa.
