Atiku ya bukaci Tinubu da ICPC su saki El-Rufai nan take

0
Atiku ya bukaci Tinubu da ICPC su saki El-Rufai nan take

Kotu ta bai wa El-Rufai belin naira miliyan 100 da tsauraran sharuɗɗa

Spread the love

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya buƙaci gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da hukumar ICPC da su gaggauta sakin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ake tsare da shi bisa wasu zarge-zargen da ake bincike a kansu. Atiku ya bayyana cewa ci gaba da tsare El-Rufai ba tare da hukunci daga kotu ba ya saɓa wa tsarin dimokuraɗiyya da adalci.

Atiku ya yi wannan kira ne yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan tsare El-Rufai da kuma sake kama shi bayan an ba shi beli a baya.

Rahotanni sun nuna cewa tsohon gwamnan na fuskantar bincike daga hukumar ICPC bayan EFCC ta fara kama shi kan wasu zarge-zargen cin hanci da rashawa.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa bai kamata a riƙa amfani da hukumomin gwamnati wajen matsin lamba ga ‘yan adawa ko masu ra’ayin sabani ba. Ya ce duk wanda ake zargi yana da damar kare kansa a gaban kotu cikin adalci, maimakon tsare shi na dogon lokaci.

A nasa ɓangaren, iyalan El-Rufai da magoya bayansa sun ci gaba da nuna damuwa kan yadda ake tafiyar da lamarin.

Hakan na zuwa ne bayan rasuwar mahaifiyar tsohon gwamnan, Hajiya Umma El-Rufai, inda aka samu rahotannin cewa an sake shi na ɗan lokaci domin halartar jana’izarta kafin daga baya aka dawo da shi tsare.

Batun dai ya ƙara jawo muhawara a fagen siyasar Najeriya, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027.

Masu sharhi na ganin rikicin siyasar tsakanin manyan ‘yan adawa da gwamnatin Tinubu na ƙara zafi, yayin da ake ci gaba da kiraye-kirayen a tabbatar da gaskiya da bin doka wajen gudanar da bincike kan manyan ‘yan siyasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *