Dr Umar Ardo ya bayyana dalilan da suka sa yake adawa da rejistar NDC da INEC tayi

0
Dr Umar Ardo ya bayyana dalilan da suka sa yake adawa da rejistar NDC da INEC tayi

Dr Umar Ardo ya bayyana dalilan da suka sa yake adawa da rejistar NDC da INEC tayi

Spread the love

Dakta Umar Ardo, daya daga cikin jagororin ƙungiyar siyasa ta ADA, ya bayyana dalilan da suka sa ya nuna adawa da yadda Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, wato INEC, na rajistar jam’iyyar (NDC). Ardo ya ce akwai kura-kurai da rashin bin ka’ida a tsarin rajistar jam’iyyar.

A cewarsa, NDC ba ta bi dukkan matakan da dokar INEC ta tanada ba kafin samun rajista a matsayin cikakkiyar jam’iyyar siyasa.

Ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta cika fom ɗin rajista na EC15A ba, sannan kuma ba ta biya kuɗin rajista na naira miliyan biyu da ake bukata domin fara tsarin tantancewa ba.

Ardo ya ƙara da cewa babu wasu muhimman takardu da aka gabatar wa kotu domin tabbatar da cewa NDC ta cika sharuddan kundin tsarin mulki da dokokin zaɓe.

Ya zargi wasu da yin amfani da umarnin kotu wajen samun rajistar jam’iyyar ba tare da cikakken bin doka ba.

Sai dai ya nuna damuwa cewa wasu manyan ‘yan siyasa kamar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso sun shiga jam’iyyar NDC, lamarin da ya sa mutane da dama suke ganin dole ne a amince da rajistar jam’iyyar duk da korafe-korafen da ake yi.

Duk da haka, Umar Ardo ya jaddada cewa ba zai amince da abin da ya kira saba doka ba, yana mai cewa zai ci gaba da kalubalantar rajistar NDC a gaban kotu domin tabbatar da gaskiya da bin doka a harkokin siyasar Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *