Kotu ta bai wa El-Rufai belin naira miliyan 100 da tsauraran sharuɗɗa

0
Atiku ya bukaci Tinubu da ICPC su saki El-Rufai nan take

Kotu ta bai wa El-Rufai belin naira miliyan 100 da tsauraran sharuɗɗa

Spread the love

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai beli na Naira miliyan 100 bayan gurfanar da shi a gaban kotu kan wasu tuhume-tuhume da ake yi masa.

Alƙaliya mai shari’a, Justice Joyce Abdulmalik, ta bayyana cewa dole ne El-Rufai ya cika wasu tsauraran sharuɗɗa kafin ya samu damar fita daga tsarewa.

Kotun ta umarci wanda zai tsaya masa ya kasance babban ma’aikacin gwamnatin tarayya mai mataki na 17 zuwa sama, sannan ya mallaki gida a yankunan Maitama ko Asokoro da ke Abuja.

Haka kuma dole ne wanda zai tsaya masa ya gabatar da takardun mallakar gidan da kuma bayanan albashinsa na watanni uku domin tabbatar da cancantarsa.

Baya ga haka, kotun ta umurci El-Rufai da ya miƙa dukkan fasfo dinsa na ƙasashen waje ga rajistrar kotu. An kuma ce dole ne ya riƙa kai kansa hedikwatar DSS a duk ranar Juma’ar ƙarshe ta wata domin sanya hannu a rajistar halarta har sai an kammala shari’ar.

Alƙaliyar ta yi gargaɗin cewa duk rashin bin sharuɗɗan da aka gindaya zai iya sa a soke belin nan take. Kotun ta kuma buƙaci wanda zai tsaya masa ya kawo takardar shaidar biyan haraji da kuma wasiƙar tabbatarwa daga ma’aikatarsa kafin a amince da belin gaba ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *