Matasa sun ƙona ofishin ƙaramar hukuma Gwarzo saboda yawaitar hare-haren ƴan bindiga
Matasa sun ƙona ofishin ƙaramar hukuma Gwarzo saboda yawaitar hare-haren ƴan bindiga
Tashin hankali ya mamaye ƙaramar hukumar Gwarzo da ke jihar Kano bayan wasu fusatattun matasa suka gudanar da zanga-zanga kan matsalar tsaro da ta addabi yankin.
Rahotanni sun bayyana cewa zanga-zangar ta fara ne cikin lumana, inda matasan suka riƙa zagaya manyan tituna suna kiran gwamnati da jami’an tsaro su kawo ƙarshen hare-haren ‘yan bindiga da suka addabi al’umma.
Shaidun gani da ido sun ce bayan zanga-zangar ta ƙara tsananta, wasu daga cikin masu zanga-zangar sun kutsa cikin harabar sakatariyar ƙaramar hukumar, inda suka banka wa wani ɓangare na ginin wuta.
Gobarar ta janyo firgici a yankin yayin da hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniya, lamarin da ya sa mutane da dama suka rika guje-guje domin tsira.
Mazauna yankin sun bayyana cewa hare-haren da ake yawan kaiwa daga ‘yan bindiga sun sa mutane ke rayuwa cikin tsoro da rashin kwanciyar hankali. Wasu sun ce sun gaji da kwana cikin fargaba saboda yadda hare-haren ke ƙaruwa ba tare da ganin matakan tsaro masu ƙarfi daga gwamnati ba.
Daga bisani jami’an tsaro sun bazama yankin domin dawo da zaman lafiya tare da hana rikicin ƙara ta’azzara.
Haka kuma, hukumomi sun fara bincike kan lamarin yayin da wasu mazauna yankin ke kira ga gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma.
