Fubara ya janye daga takarar Gwamnan Rivers a APC
Fubara ya janye daga takarar Gwamnan Rivers a APC
Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya sanar da janyewarsa daga takarar gwamna ta shekarar 2027 karkashin jam’iyyar APC.
Rahotanni sun bayyana cewa Fubara ya dauki wannan mataki ne bayan doguwar takaddama da rikice-rikicen siyasa da suka dabaibaye jihar cikin ‘yan watannin nan.
A cikin sanarwar da aka wallafa, Fubara ya bayyana cewa ya yanke shawarar ne domin kare zaman lafiya da hadin kan jihar Rivers, yana mai cewa siyasa bai kamata ta zama hanyar haddasa rikici ko rarrabuwar kawuna ba. Ya kuma gode wa magoya bayansa bisa goyon bayan da suka nuna masa tun bayan hawansa mulki.
Janyewar tasa ta haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin magoya bayan APC da sauran ‘yan siyasa a jihar, inda wasu ke ganin matakin zai sauya yanayin siyasar Rivers gaba daya kafin zaben 2027.
Masu sharhi kan harkokin siyasa sun bayyana cewa wannan mataki na iya bude kofar sabbin masu neman kujerar gwamna a jam’iyyar.
Tun bayan rikicin siyasa tsakanin Fubara da wasu manyan jiga-jigan siyasa a Rivers, ana ci gaba da samun sauye-sauye a tsarin siyasar jihar. Yanzu dai hankalin jama’a ya karkata kan yadda jam’iyyun siyasa za su tsara tafiyarsu gabanin babban zaben shekarar 2027.
