Kotu ta daure mahaifiya da ƴar uwar fitaccen dan ta’adda Battujo shekara 40 a gidan yari

0
Battujo

Kotu ta daure mahaifiya da ƴar uwar fitaccen dan ta’adda Battujo shekara 40 a gidan yari

Spread the love

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa Safiya Salihu da Halima Abdullahi, mahaifiya da ‘yar uwar marigayi shugaban ‘yan ta’adda Kachallah Ibrahim Battujo, hukuncin daurin shekaru 40 a gidan yari bayan sun amsa laifukan da suka shafi taimakawa ayyukan ta’addanci.

Kotun ta same su da laifin isar da bayanai ga Battujo ta hanyar waya da kuma boye muhimman bayanai game da ayyukansa duk da sanin cewa jami’an tsaro na nemansa. Haka kuma an tabbatar da cewa sun san yana da makamai amma ba su sanar da hukumomi ba.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Hauwa Joseph Yilwa, ta yanke hukuncin ne bayan wadanda ake tuhuma sun amsa wasu daga cikin tuhume-tuhumen da gwamnatin tarayya ta gabatar a kansu, yayin da aka yi watsi da wasu tuhume-tuhume biyu bisa bukatar masu gabatar da kara.

Hukuncin ya zo ne kwanaki kadan bayan jami’an tsaro sun kashe Battujo a wani samame da suka kai a dajin Iluke da ke karamar hukumar Kabba/Bunu ta jihar Kogi, lamarin da ke nuna ci gaba da matsin lamba kan masu hannu a ayyukan ta’addanci a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *