PDP ta miƙa tikitin sanata ga Iyabo Obasanjo bayan ficewarta daga APC
PDP ta miƙa tikitin sanata ga Iyabo Obasanjo bayan ficewarta daga APC
Jam’iyyar PDP a Jihar Ogun ta karɓi tsohuwar Sanata Iyabo Obasanjo cikin jam’iyyar bayan ficewarta daga APC, tare da ba ta tikitin takarar Sanatan Ogun ta tsakiya gabanin zaɓen 2027.
Iyabo Obasanjo, ‘yar tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, ta dawo PDP ne bayan ta yi murabus daga APC sakamakon rashin gamsuwa da yadda aka gudanar da harkokin cikin jam’iyyar da zaɓen ɗan takararta na gwamna.
A wajen taron karɓar ta da aka yi a Abeokuta, shugabannin PDP sun bayyana ta a matsayin ‘yar takarar jam’iyyar ta Ogun Central, yayin da ita kuma ta sha alwashin yin aiki da gaskiya da biyayya ga jam’iyyar.
Ta kuma bayyana cewa za ta fafata da ƙarfi a zaɓen 2027, tana mai cewa tana da ƙwarewa da gogewar da za su taimaka wajen wakiltar al’ummar mazabar Ogun ta tsakiya yadda ya kamata.
