Shahararriyar Ƴar TikTok Fati Cele ta shiga hannun ƴan sanda bayan mutuwar saurayinta a gidanta
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta tsare fitacciyar ’yar TikTok, Fati Cele, bayan rasuwar saurayinta Isma’il Makaye a gidanta da ke unguwar Danbare. Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da kama ta tare da bayyana cewa bincike na ci gaba da gudana.
Rahotanni sun nuna cewa Fati Cele ta tayar da ƙarar neman agaji bayan wata matsala da ta faru a gidanta, lamarin da ya sa aka garzaya da Isma’il zuwa Asibitin Nassarawa, inda daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa.
Bayan faruwar lamarin, jami’an ’yan sanda daga ofishin Dorayi Babba suka ɗauki Fati Cele zuwa tsare domin taimaka wa bincike kan hakikanin musabbabin mutuwar saurayin nata.
Marigayin, wanda ɗan kasuwar kayan kwalliya ne a Kano, an yi masa jana’iza bayan an miƙa gawarsa ga iyalansa.
