Iran ta musanta karɓar kuɗin wucewa daga tankokin mai na Indiya
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian
Ƙasar Iran ta musanta zargin cewa tana karɓar kuɗin fito daga jiragen dakon mai na ƙasar India da ke wucewa ta mashigin ruwan Hormuz, tana mai cewa babu wani irin haraji da aka kakaba musu.
Jakadan Iran a Indiya, Mohammad Fathali, ya bayyana cewa tankokin man Indiya da suka ratsa yankin ba su biya ko sisi ba, yana mai ƙalubalantar duk wanda ke da shakka da ya tuntubi gwamnatin Indiya domin tabbatar da hakan.
Wannan martani na Iran ya biyo bayan zarge-zargen da suka fito daga shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya yi barazanar hana duk wani jirgin ruwa wucewa idan har ya biya irin wannan kuɗi ga Iran.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa Indiya ma ta musanta biyan kuɗin, inda ta ce wasu jiragenta sun ratsa mashigin ba tare da wata matsala ba, duk da tashin hankali da ke faruwa a yankin.
Mashigin ruwan Hormuz na da matuƙar muhimmanci ga harkokin man fetur na duniya, kuma rikicin da ke faruwa a yankin na ci gaba da jefa fargaba kan zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma tasirin hakan ga tattalin arzikin duniya.
