Taraba ta amince da Naira biliyan daya don biyan WAEC da NECO ga dalibai
Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas
Gwamnatin Jihar Taraba ta amince da ware Naira biliyan daya domin biyan kudin jarrabawar WAEC da NECO ga ɗaliban makarantun gwamnati a faɗin jihar.
Wannan mataki na daga cikin shirin gwamnati na rage nauyin kuɗin jarrabawa a kan iyaye tare da inganta damar samun ilimi ga ɗalibai.
Rahotanni sun bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da cewa babu wani ɗalibi da zai fuskanci matsalar rashin kuɗin rubuta jarrabawa a jihar.
Gwamnatin ta ce shirin zai taimaka wajen ƙara yawan ɗaliban da ke kammala makarantar sakandare cikin nasara.
Haka kuma, an bayyana cewa wannan tallafi na daga cikin manyan manufofin gwamnatin jihar na inganta ilimi da ci gaban matasa.
