Fasahar AI zai taimaka wajen magance ƙalubalen Najeriya – Pantami
Farfesa Isa Ali Pantami
Tsohon Ministan Sadarwa na Najeriya, Isa Ali Pantami, ya bayyana cewa fasahar zamani musamman AI na iya zama muhimmin mafita wajen magance kalubalen da ƙasar ke fuskanta.
Pantami ya yi wannan bayani ne yayin da yake jawabi kan muhimmancin amfani da fasaha wajen inganta rayuwar al’umma, inda ya ce Najeriya na da damar cin gajiyar sauye-sauyen fasaha idan ta yi amfani da su yadda ya kamata wajen cigaban tattalin arziki da zamantakewa.
Ya kara da cewa AI da sauran sabbin fasahohi za su iya taimakawa a fannoni da dama kamar ilimi, kiwon lafiya, tsaro da kuma harkokin kasuwanci, musamman idan aka samu ingantaccen tsarin aiwatar da su da kuma horar da matasa.
A cewarsa, duk da cewa fasaha na zuwa da kalubale, idan aka sarrafa ta yadda ya dace za ta zama babban kayan aiki wajen rage talauci, ƙirƙirar ayyukan yi da kuma inganta yadda gwamnati ke gudanar da ayyukanta.
Pantami ya jaddada cewa Najeriya na bukatar saka hannun jari sosai a fannin fasaha, tare da ƙarfafa kirkire-kirkire a tsakanin matasa domin su taka rawar gani a zamanin dijital da ke ƙara sauyawa cikin sauri a duniya.
