Ana fargabar asarar rayuka bayan arangamar tsakanin Lakurawa da ‘Yan bindiga a Neja
Ana fargabar mutane da dama sun mutu bayan wata mummunar arangama da ta ɓarke tsakanin mayaƙan Lakurawa da wasu ’yan bindiga a yankin Tapkin Giyayya da ke ƙaramar hukumar Mashegu a Jihar Neja.
Rahotanni sun ce rikicin ya samo asali ne bayan wasu ’yan bindiga sun kutsa daga dazukan Jihar Zamfara zuwa yankin Mashegu, lamarin da ya janyo musayar wuta mai tsanani tsakanin ɓangarorin biyu.
Mazauna yankin sun bayyana cewa an ga gawarwaki da dama yayin da wasu da suka jikkata suka tsere daga wurin, sai dai har yanzu ba a tantance adadin waɗanda suka mutu ba.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba, yayin da ake ci gaba da bibiyar halin da ake ciki.
