Babu shugaban da ya kaddamar da ayyuka masu yawa kamar Tinubu a tarihi – Akpabio

0
Babu shugaban kasa da ya kaddamar da ayyuka masu yawa kamar Tinubu - Akpabio

Babu shugaban kasa da ya kaddamar da ayyuka masu yawa kamar Tinubu - Akpabio

Spread the love

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce babu wani Shugaban Ƙasa a tarihin Najeriya da ya kaddamar da ayyukan raya ƙasa masu yawa kamar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Akpabio ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da wasu ayyukan ci gaba a Babban Birnin Tarayya, inda ya ce gwamnatin Tinubu ta nuna ƙuduri wajen samar da manyan ababen more rayuwa domin inganta rayuwar al’umma.

Ya kuma yabawa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, kan yadda yake aiwatar da ayyukan ci gaba cikin sauri, yana mai cewa sauye-sauyen da ake gani a Abuja shaida ce ta ingantaccen jagoranci.

Sai dai kalaman Akpabio na ci gaba da haifar da muhawara tsakanin masu goyon bayan gwamnati da masu adawa, inda kowane bangare ke bayyana ra’ayinsa kan irin nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *