Shugaba Tinubu ya buƙaci haɗin kan yan Najeriya domin ci gaban ƙasa

0
Shugaba Tinubu ya buƙaci haɗin kan yan Najeriya domin ci gaban ƙasa

Bola Ahmad Tinubu

Spread the love

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta sassauta ƙoƙarinta na bunƙasa ƙasar nan ba, yana mai kira ga ‘yan Najeriya su haɗa kai da gwamnati wajen gina ƙasa mai ci gaba. Ya yi wannan furuci ne a Abuja yayin ƙaddamar da wasu ayyukan tituna a Babban Birnin Tarayya.

Tinubu ya ce gwamnatinsa ta kawo ƙarshen al’adar barin ayyukan raya ƙasa ba a kammala su ba, tare da jaddada cewa za a ci gaba da zuba jari a ayyukan more rayuwa domin inganta tattalin arziki da samar da guraben ayyukan yi.

Shugaban ya yaba wa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, bisa yadda yake jagorantar aiwatar da ayyukan ci gaba a Abuja, yana mai cewa sakamakon aiki ne ke nuna ingancin shugabanci ba yawan alkawura ba.

Har ila yau, Tinubu ya buƙaci mazauna Abuja da shugabannin al’umma su kare kadarorin gwamnati tare da cika wajibcin biyan haraji da kuɗaɗen ƙasa domin bai wa gwamnati damar aiwatar da ƙarin ayyukan raya ƙasa a nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *