Zargin lalata da Ɗaliba ya bankado babban gibin da ake dashi na tsaron yara a Makarantun Bauchi

0
Zargin lalata da Ɗaliba ya bankado babban gibin da ake dashi na tsaron yara a Makarantun Bauchi

Zargin lalata da Ɗaliba ya bankado babban gibin da ake dashi na tsaron yara a Makarantun Bauchi

Spread the love

Wani bincike da ƙungiyar WE AID INITIATIVE ta gudanar ya nuna cewa akwai babban gibin tsarin kariyar yara a wasu makarantu a Jihar Bauchi, bayan zargin da ake yi cewa wani shugaban makaranta a unguwar Yelwa ya yi lalata da wata ɗaliba mai shekara shida.

An miƙa lamarin ga Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya domin ci gaba da bincike.

Rahoton binciken ya bayyana cewa makarantar ba ta da ingantattun manufofi da ƙa’idojin kare yara, hanyoyin kai rahoton cin zarafi ko kuma tsarin cikin gida na magance irin waɗannan matsaloli, abin da ya nuna raunin tsarin kariya a makarantar.

Bayan binciken, ƙungiyar ta tattauna da Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci gaban Yara ta Jihar Bauchi, inda aka bayyana cewa jihar ba ta da cikakken tsarin manufofin kariyar yara da zai zama jagora ga makarantu da sauran cibiyoyin da ke kula da yara.

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnati da masu ruwa da tsaki su gaggauta samar da ingantaccen tsarin kariyar yara a makarantu domin kare ɗalibai daga cin zarafi, ƙarfafa amincewar iyaye da kuma tabbatar da cewa yara na karatu cikin muhalli mai aminci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *