’Yan uwan mayakan ISWAP su shida sun mika wuya ga sojoji a Borno

0
 ’Sojoji sun hallaka ’yan Boko Haram 25 bayan dakile hari a sansanin sojoji a Borno

Sojoji sun hallaka ’yan Boko Haram 25 bayan dakile hari a sansanin sojoji a Borno

Spread the love

Wasu ’yan uwa shida na mayakan kungiyar ISWAP sun mika wuya ga dakarun Sojojin Najeriya a garin Pulka, karamar hukumar Gwoza ta Jihar Borno, bayan sun tsere daga wani maboyar ’yan ta’addan da ke Bulakambula a karamar hukumar Bama.

Rahoton ya ce sun mika wuya ne ga dakarun Operation Hadin Kai a ranar 28 ga Satumba, 2026.

Wani masani kan harkokin yaki da ta’addanci, Zagazola Makama, ya bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa mutanen sun tsere ne daga maboyar ISWAP kafin su isa yankin da dakarun gwamnati ke iko da shi.

Daga bisani an mika su ga jami’an Grassroots Initiative for Strengthening Community Resilience (GISCOR) a Pulka domin ba su tallafi da kuma gudanar da sauran matakan da suka dace.

A wani makamancin ci gaba, dakarun Sojojin Najeriya sun kuma ceto wata yarinya karama da ake zargin ’yar wani mayakin ISWAP ce a kauyen Hudugum, kan hanyar Gwoza zuwa Limankara.

Rahoton ya ce yarinyar ta tsere ne daga wata maboya ta ’yan ta’addan da ke yankin tsaunukan Mandara, kafin daga bisani a mika ta ga hukumomin sansanin ‘yan gudun hijira na Gwoza domin kula da ita.

Wadannan abubuwan sun zo ne yayin da dakarun Operation Hadin Kai ke ci gaba da gudanar da ayyukan soji da leken asiri a yankunan Gwoza da kewaye.

A cewar rahoton, tserewar mutanen da ke da alaka da mayakan ISWAP daga maboyarsu zuwa wuraren da jami’an tsaro ke iko da su na nuna yadda ake ci gaba da matsa wa kungiyoyin ’yan ta’adda lamba a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *