Lokacin gyaran tattalin arziki ya wuce, yanzu lokacin inganta rayuwar ‘yan Najeriya ne – Tinubu
Tinubu ya yi murna yayin da kuɗin sufuri ya ragu da Naira 1,000 a Abuja
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa kasar ta kammala wani muhimmin mataki na gyaran tattalin arziki, inda yanzu gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen samar da yalwar arziki da inganta rayuwar ’yan Najeriya.
Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabinsa na ranar samun ’Yancin Najeriya karo na 66 a ranar Alhamis, ya ce manufar gwamnati a wannan sabon mataki ita ce tabbatar da wadatar arziki wadda za ta amfani al’umma baki daya.
Shugaban ya ce gwamnati za ta mayar da hankali wajen rage tsadar rayuwa ta hanyar rage kudin samar da kayayyaki da safarar su, tare da bunkasa noma, masana’antu, makamashi da samar da ayyukan yi ga matasa.
Tinubu ya kuma ce duk da cewa matsalolin tattalin arzikin Najeriya sun samo asali ne daga shekaru masu yawa, ba za a iya magance dukkan su cikin shekaru hudu ba, amma ya jaddada cewa an gyara alkiblar tattalin arzikin kasar kuma yanzu lokaci ya yi na gina makoma mai kyau.
