Yari ya gana da Tinubu kan shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen APC
Yari ya gana da Tinubu kan shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen APC
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Daraktan-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC, Abdulaziz Yari, ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Legas, inda suka tattauna kan shirye-shiryen jam’iyyar gabanin zaɓen shekarar 2027.
Yari ya bayyana cewa ya gana da Tinubu ne tare da ɗansa Ahmad, inda suka tattauna yadda shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen ke gudana da kuma matakan da ya kamata a ɗauka domin ƙarfafa haɗin kan APC gabanin babban zaɓen na 2027.
A cewar Yari, tattaunawar ta kuma mayar da hankali kan yadda za a tabbatar da cewa jam’iyyar ta kasance cikin haɗin kai tare da inganta tsarinta domin tunkarar zaɓen.
Wannan na zuwa ne yayin da kwamitin yaƙin neman zaɓen APC ke gudanar da shawarwari da ganawa da masu ruwa da tsaki a sassa daban-daban na ƙasar.
A baya, Yari ya bayyana cewa APC za ta fi mayar da hankali wajen gabatar da ayyukan da gwamnatin Tinubu ta aiwatar a matsayin wani ɓangare na yaƙin neman zaɓen 2027, maimakon dogaro da sababbin alkawura.
Ya kuma ce ƙarfafa haɗin kan jam’iyyar zai kasance cikin muhimman abubuwan da za su jagoranci shirye-shiryen ta.
