Bafarawa ya kafa wa Tinubu Sharaɗin samun zaman lafiya kafin ya samu kuri’unsa a 2027
Bafarawa ya kafa wa Tinubu Sharaɗin samun zaman lafiya kafin ya samu kuri’unsa a 2027
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya bayyana cewa a shirye yake ya zaɓi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027, matuƙar ya samar da cikakken tsaro da dawo da zaman lafiya a jihar Sokoto da sauran yankunan Arewacin Najeriya.
Bafarawa ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da gidan rediyon Faransa, RFI, inda ya jaddada cewa samar da tsaro shi ne babban sharadin da zai sa ya goyi bayan Tinubu a zaɓe mai zuwa.
Bafarawa ya ce lokaci ya kusa ƙurewa ga shugaban ƙasar, yana mai cewa yana da iko, kuɗi da jami’an tsaron da za su iya shawo kan matsalar rashin tsaro a Arewa cikin wata ɗaya zuwa uku idan aka mayar da hankali wajen magance matsalar.
Ya kuma bayyana cewa ba ya neman kuɗin kamfe ko wata alfarma daga Tinubu, sai dai yana son a tabbatar da tsaro domin jama’a su koma gudanar da harkokinsu na yau da kullum, musamman zuwa makarantu, noma da kasuwanci.
Tsohon gwamnan ya nuna damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ta hana yara da dama zuwa makaranta, manoma zuwa gonakinsu, tare da tilasta wa mazauna wasu garuruwa barin gidajensu sakamakon hare-haren ‘yan bindiga.
Ya kuma bayyana cewa shi ba ɗan jam’iyyar APC ba ne, amma duk wanda ya samar da zaman lafiya a Arewa, ciki har da Tinubu, zai iya samun goyon bayansa.
Bafarawa ya ƙara da cewa tun bayan da Tinubu ya zama shugaban ƙasa, sau ɗaya kacal suka haɗu a wani masallaci, yana mai zargin cewa wani mutum da aka ce zai taimaka masa ya gana da shugaban ƙasar daga baya ya ƙi yin hakan tare da toshe lambobin wayarsa.
A wani ɓangare na hirar, Bafarawa ya kare tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari, kan amincewarsa da zama daraktan yaƙin neman zaɓen Tinubu na 2027, duk da matsalar hare-haren ‘yan bindiga da ke addabar jihar Zamfara.
Ya ce Yari ɗan APC ne, don haka yana da damar bin shawarar jam’iyyarsa da kuma mutunta naɗin da shugaban ƙasa ya yi masa.
Bafarawa ya bayyana cewa Yari ya nemi shawarwarin wasu mutane kafin ya amince da naɗin, sannan ya sake komawa gare su bayan an naɗa shi, lamarin da ya ce yana nuna nagartarsa.
