Tinubu ya tura Ribadu, IGP da manyan jami’ai zuwa Oyo bayan garkuwa da dalibai da malamai
Tinubu ya tura Ribadu, IGP da manyan jami'ai zuwa Oyo bayan garkuwa da dalibai da malamai
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aika wata babbar tawaga ta gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Nuhu Ribadu zuwa wasu ƙauyukan Jihar Oyo da suka fuskanci hare-haren masu garkuwa da mutane, domin duba halin da ake ciki tare da ƙarfafa matakan ceto waɗanda har yanzu suke hannun masu garkuwa.
Tawagar ta ƙunshi manyan jami’an tsaro da gwamnati ciki har da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda da wasu ministoci, inda suka gana da iyalan waɗanda aka sace tare da shugabannin al’umma domin jin koke-kokensu da kuma tabbatar musu da cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kubutar da waɗanda aka yi garkuwa da su.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindiga sun kai hari kan makarantu da wasu al’ummomi a yankin Ogbomoso na Jihar Oyo, inda suka yi awon gaba da dalibai, malamai da shugaban makaranta, lamarin da ya haifar da fargaba da zanga-zangar neman daukin gaggawa daga jama’a.
A yayin ziyarar, jami’an gwamnatin tarayya sun tabbatar da cewa ana gudanar da ayyukan bincike da ceto cikin hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro na tarayya da na jihar, tare da jaddada cewa za a ci gaba da matsa lamba har sai an ceto dukkan mutanen da aka sace.
Shugaba Tinubu ya kuma sake tabbatar wa iyalan waɗanda abin ya shafa cewa gwamnati na aiki dare da rana domin ganin an dawo da su gida lafiya, yana mai cewa ba za a manta da su ba kuma za a ɗauki ƙarin matakan kare makarantu da al’ummomin da ke cikin haɗari a faɗin ƙasar nan.
