Hare-haren Boko Haram sun zama barazana ga rayukan jama’ar Hong – Inuwa Waganda

0
Hare-haren Boko Haram sun zama barazana ga rayukan jama’ar Hong – Inuwa Waganda

Hare-haren Boko Haram sun zama barazana ga rayukan jama’ar Hong – Inuwa Waganda

Spread the love

Shugaban Karamar Hukumar Hong a Jihar Adamawa, Inuwa Usman Wa’aganda, ya bayyana damuwa matuka kan yadda hare-haren kungiyar Boko Haram suka zama ruwan dare a yankin, yana mai cewa al’ummar karamar hukumar na ci gaba da rayuwa cikin fargaba sakamakon matsalar tsaro da ke addabar su.

Wa’aganda ya ce wasu kauyuka da ke kusa da yankunan da ke iyaka da dazuzzuka na fuskantar barazanar hare-hare akai-akai, lamarin da ke hana mazauna yankin gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin kwanciyar hankali. Ya kara da cewa matsalar na shafar noma, kasuwanci da sauran hanyoyin samun abin masarufi.

Shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa duk da kokarin jami’an tsaro wajen dakile hare-haren, har yanzu akwai bukatar kara yawan jami’an tsaro da kayan aiki domin magance matsalar gaba daya. Ya ce hare-haren na ci gaba da jefa jama’a cikin tashin hankali da asarar dukiyoyi.

Haka kuma, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da su dauki matakan gaggawa wajen karfafa tsaro a yankin domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma. A cewarsa, samar da ingantaccen tsaro ne kadai zai dawo da zaman lafiya da ci gaban yankin.

Wa’aganda ya tabbatar da cewa al’ummar Hong na ci gaba da bukatar tallafi da kulawar gwamnati, yana mai jaddada cewa idan ba a dauki kwararan matakai ba, matsalar na iya kara tsananta tare da janyo karin matsalolin jin kai da tattalin arziki ga mazauna yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *