Ragin Farashin Man Fetur da Tinubu ya yi na kwana 30 zuwa N1,350 dabarar siyasa ce – Atiku

0
Ragin Farashin Man Fetur da Tinubu ya yi na Kwana 30 zuwa N1,350 ‘Dabarar siyasa ce’ - Atiku

Ragin Farashin Man Fetur da Tinubu ya yi na Kwana 30 zuwa N1,350 ‘Dabarar siyasa ce’ - Atiku

Spread the love

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi kakkausar suka ga shirin Gwamnatin Tarayya na rage farashin man fetur na tsawon kwanaki 30 a gidajen man NNPC, yana mai bayyana matakin a matsayin wata dabara ta neman farin jini da aka dauka cikin rudani sakamakon matsin lambar da al’ummar ƙasar ke fuskanta.

A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar ADC, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Alhamis, Atiku ya ce bai dace gwamnati ta yi amfani da rangwamen man fetur na ɗan lokaci a matsayin abin jan hankalin ’yan Najeriya ba, bayan da suka shafe shekaru suna fama da tsadar man fetur da hauhawar farashin kayayyaki.

Atiku ya ce abin da gwamnati ke shirin yi ba zai magance matsalar tattalin arzikin ƙasa ba, domin da zarar kwanaki 30 sun cika, ’yan Najeriya za su koma fuskantar irin tsadar man fetur, hauhawar kuɗin sufuri da tashin farashin kayan abinci da suka addabe su.

Ya bayyana matakin a matsayin “maganin wucin gadi” ga wata babbar matsalar da gwamnati da kanta ta taimaka wajen haifarwa.

Ya kuma nuna damuwa kan cewa rangwamen zai kasance ne kawai a gidajen man NNPC, yayin da gwamnati ba ta bayyana adadin kuɗin da za a rage wa mai mota kan kowace lita ba, ko kuma ta tabbatar da cewa masu motocin haya za su mayar da rangwamen ga fasinjoji ta hanyar rage kuɗin sufuri.

Atiku, ya ce sauya matsayar gwamnati kwatsam kan wannan batu na jin daɗin al’umma na nuna cewa ta fahimci girman wahalar da ’yan Najeriya ke ciki.

Ya kuma sake jaddada buƙatarsa ta samar da tsarin tallafin samar da man fetur da aka tsara cikin kasafin kuɗi, wanda za a danganta shi da man da aka tace a cikin Najeriya, domin rage farashi da kuma ƙarfafa matatun man cikin gida.

Atiku ya ce abin da ’yan Najeriya ke buƙata shi ne sauƙi mai ɗorewa, ba rangwamen kwanaki 30 da zai ƙare sannan wahala ta dawo ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *