Hadimin Atiku ya zargi Tinubu da satar shawarar Atiku na dawo da tallafin Man Fetur

0
Atiku ya zargi Tinubu da yin watsi da ’yan sandan da suka yi ritaya

Atiku ya zargi Tinubu da yin watsi da ’yan sandan da suka yi ritaya

Spread the love

Demola Olarewaju, babban mataimaki kan harkokin siyasa ga tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da karɓo shawarar ubangidansa kan rage farashin man fetur ta hanyar tallafi, bayan Gwamnatin Tarayya ta sanar da sabon tsarin sayar da fetur ba tare da riba ba a gidajen mai na NNPC.

Olarewaju ya bayyana cewa Tinubu ya kamata ya gode wa Atiku bisa shawarar da ya ce gwamnati ta karɓa, tare da sauya mata suna.

Ya kuma buƙaci Shugaban Ƙasar da ya shirya barin fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock cikin lumana a shekarar 2027, yana mai cewa ’yan Najeriya za su yanke hukunci ta hanyar zaɓe.

Mataimakin na Atiku ya bayyana hakan ne bayan Ministan Kuɗi kuma mai kula da Tattalin Arziƙi, Taiwo Oyedele, ya sanar da cewa NNPC za ta sayar da fetur kan farashin da ta saya ba tare da ƙara ribar dillanci ba, na tsawon kwanaki 30.

Gwamnatin Tarayya ta ce matakin na da nufin rage wa al’umma raɗaɗin tsadar man fetur, musamman masu ƙaramin ƙarfi da masu sufuri.

Sai dai Atiku ya sha sukar matakin, yana mai cewa rage farashin na wata guda ba zai magance matsalolin tsadar rayuwa na dogon lokaci ba.

Ya jaddada buƙatar samar da tsarin tallafin da zai taimaka wajen rage farashin man fetur da aka tace a cikin gida, yana mai cewa ’yan Najeriya na buƙatar mafita mai ɗorewa maimakon sauƙin da zai ƙare bayan kwanaki 30.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *