Gwamnati ta sanar da rage farashin man fetur na kwanaki 30 domin samun sauƙi ga ’yan Najeriya
Gwamnati ta sanar da rage farashin man fetur na kwanaki 30 domin samun sauƙi ga ’yan Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta sanar da bayar da rangwame kan man fetur da ake sayarwa a gidajen mai na Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPC) a faɗin Najeriya, na tsawon kwanaki 30, domin rage wa ’yan ƙasa raɗaɗin tsadar man fetur.
Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziƙi, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan, inda ya ce gwamnati za ta sayar da man fetur ɗin ne kan farashin da ya kai mata, ba tare da ƙara wani riba a kai ba.
Ya kuma bayyana cewa wannan matakin ba tallafin man fetur ba ne, sai dai rangwame ne da gwamnati ta ƙaddamar na ɗan lokaci.
Oyedele ya ce za a bai wa motocin sufuri na jama’a fifiko wajen cin moriyar rangwamen, domin matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na rage tasirin tsadar man fetur ga harkokin sufuri da rayuwar yau da kullum ta ’yan Najeriya.
Gwamnatin ta bayyana cewa rangwamen zai fara aiki na tsawon kwanaki 30, yayin da ake sa ran matakin zai taimaka wajen rage wasu daga cikin matsalolin da hauhawar farashin man fetur ke haifarwa ga al’umma da harkokin sufuri a ƙasar.
