Atiku ya zargi Gwamnatin Tinubu da yin watsi da manoma yayin da shigo da abinci ke karuwa daga waje

0
Atiku ya bukaci INEC ta bayyana kamfanonin da za su buga kayan zaɓen 2027

Atiku ya bukaci INEC ta bayyana kamfanonin da za su buga kayan zaɓen 2027

Spread the love

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da yin watsi da manoman Najeriya, yayin da ake ci gaba da shigo da kayan abinci daga ƙasashen waje.

Atiku ya ce hakan na faruwa ne yayin da manoma ke fuskantar matsalar rashin tsaro da kuma tsadar samar da amfanin gona.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Sadarwa na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen ADC, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce kasuwancin kayan amfanin gona na Najeriya ya sauya daga samun rarar N740.27 biliyan a rabin farko na shekarar 2025 zuwa gibin N56.13 biliyan a makamancin lokacin na 2026.

Ya ce wannan na nufin an samu sauyin kusan N796.40 biliyan cikin shekara guda, yayin da fitar da kayan amfanin gona zuwa ƙasashen waje ta ragu da kashi 33.3 cikin 100.

Atiku ya ce Najeriya na ci gaba da fitar da albarkatun noma kamar ƙwayar cashew da koko ba tare da sarrafa su yadda ya kamata a cikin gida ba, lamarin da yake hana ƙasar samun cikakken ribar da za ta samu daga waɗannan kayayyaki.

Ya kuma soki matakan gwamnatin tarayya na rage radadin matsalar man fetur, musamman shirin CNG, yana mai cewa tsadar sauya motoci zuwa CNG da ƙarancin kayan sauyawar na hana talakawa cin gajiyarsa.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce idan aka ba shi damar jagorantar Najeriya, gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen ƙarfafa manoma da masana’antun sarrafa amfanin gona, tare da samar da tallafin samar da kayayyaki a cikin gida.

Ya ce manufarsa ita ce a noma amfanin gona a Najeriya, a sarrafa shi a Najeriya, a samar da ayyukan yi a Najeriya, sannan a rage dogaro da kayayyakin da ake shigo da su daga ƙasashen waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *