NDC ta keɓe Obi da Kwankwaso daga rantsuwar hana sauya sheƙa
Peter Gregory Obi, Rabi'u Musa kwankwaso
Jam’iyyar NDC ta sanar da keɓe ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2027, Peter Obi da abokin takararsa Rabiu Musa Kwankwaso daga sabuwar rantsuwar hana sauya sheƙa da ta tanada wa sauran masu neman mukaman zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar.
Jam’iyyar ta ce manufar rantsuwar ita ce hana zaɓaɓɓun jami’anta barin jam’iyyar bayan sun samu nasara a zaɓe, domin kare haɗin kai da kuma tabbatar da biyayya ga manufofin NDC.
Sai dai shugabannin jam’iyyar sun bayyana cewa Obi da Kwankwaso ba za su shiga wannan tsarin ba saboda matsayinsu na musamman a matsayin masu jagorantar tikitin shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027.
Matakin ya janyo ce-ce-ku-ce a fagen siyasa, inda wasu ke ganin keɓewar na nuna fifiko ga manyan jagororin jam’iyyar, yayin da NDC ke ƙoƙarin tabbatar da tsayuwar daka da haɗin kan mambobinta gabanin babban zaɓen 2027.
