Mustapha Salihu ya bayyana shirin tsayawa takarar Gwamnan Adamawa a 2027

0
Rikici ya kaure a APC kan takarar Mustapha Salihu na sanatan Adamawa ta tsakiya - Isma'il

Comrade Mustafa Salihu

Spread the love

Comrade Mustapha Salihu ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Adamawa a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2027, inda ya jaddada kudurinsa na kawo sauyi mai ma’ana a harkokin mulki da ci gaban jihar.

Ya ce ya ɗauki wannan mataki ne domin bayar da gudunmawa wajen inganta rayuwar al’umma tare da bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga matasa.

Salihu ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a Yola, inda ya kuma nemi goyon bayan ‘yan jam’iyya da al’ummar jihar baki ɗaya.

Ya tabbatar da cewa idan aka ba shi dama, zai mayar da hankali kan tsaro, ilimi, lafiya da bunƙasa ababen more rayuwa domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a Adamawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *