Mun san sauye-sauyenmu sun kara wa yan Najeriya talauci, Amma Bamu da zaɓi ya zama dole – Fadar Shugaban Ƙasa

0
Tinubu ya sauya tsarin INEC tare da naɗa sabbin Kwamishinoni shida gabanin zaɓen 2027

Tinubu ya sauya tsarin INEC tare da naɗa sabbin Kwamishinoni shida gabanin zaɓen 2027

Spread the love

Fadar Shugaban Ƙasa ta amince cewa sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar sun sa ƙarin ’yan Najeriya suka faɗa cikin talauci, amma ta ce babu wata hanya da gwamnati za ta samu ci gaba ba tare da ɗaukar irin waɗannan matakai masu tsauri ba.

Daniel Bwala, mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan harkokin sadarwa da manufofi, ne ya bayyana hakan.

Bwala ya yi wannan bayani ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television, inda yake kare matakan da gwamnatin Tinubu ta ɗauka tun bayan hawanta mulki a 2023, musamman cire tallafin man fetur da daidaita tsarin kasuwar canjin kuɗaɗen waje. Ya ce irin waɗannan sauye-sauye ba sa zuwa ba tare da wahala ga jama’a ba.

Ya ce kafin fara sauye-sauyen, Najeriya ta riga ta fuskanci matsalolin tattalin arziki da talauci, amma gwamnati ta ga cewa dole ne a ɗauki matakan da suka dace domin gyara matsalolin da suka daɗe suna addabar tattalin arzikin ƙasar.

Bwala ya amince cewa mutane da dama sun shiga cikin talauci sakamakon sauye-sauyen, amma ya ce gwamnati ta samu wasu ci gaba tun lokacin da aka fara aiwatar da su.

A cewarsa, gwamnati na ganin cewa sauye-sauyen sun fara haifar da wasu nasarori bayan matsalolin farko, kuma ta ci gaba da yin ƙoƙari wajen rage illolin da jama’a ke fuskanta.

Ya ce ba za a iya yin watsi da wahalhalun da ’yan Najeriya suka shiga ba, amma gwamnati na ganin matakan da ta ɗauka sun kasance wajibi domin samar da ci gaba mai ɗorewa ga tattalin arzikin ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *