Masu Karɓar Fansho a Taraba sun yi zanga-zanga, inda suka nemi a cire sakataren Gwamnatin Jihar

0
Masu Karɓar Fansho a Taraba sun yi zanga-zanga, inda suka nemi a cire sakataren Gwamnatin Jihar

Masu Karɓar Fansho a Taraba sun yi zanga-zanga, inda suka nemi a cire sakataren Gwamnatin Jihar

Spread the love

Mambobin Ƙungiyar Masu Karɓar Fansho ta Ƙasa (National Union of Pensioners), reshen Jihar Taraba, sun gudanar da zanga-zanga a Jalingo, inda suka bukaci Gwamnan Jihar, Dakta Agbu Kefas, da ya gaggauta daukar mataki kan matsalolin da suka shafi walwala da hakkokinsu na fansho.

Masu zanga-zangar sun ce an dade ana watsi da bukatunsu tun bayan ƙirƙirar Jihar Taraba a shekarar 1991.

Ƙungiyar ta kuma bayyana rashin amincewarta da Sakataren Gwamnatin Jihar, Chief Gebon Timothy Kataps Esq., inda ta zarge shi da tsoma baki a harkokin shugabancin ƙungiyar masu karɓar fansho a jihar.

Saboda haka, mambobin ƙungiyar sun gabatar da ƙuri’ar rashin amincewa da shi tare da neman Gwamna Kefas ya cire shi daga mukaminsa nan take.

Bugu da ƙari, masu karɓar fanshon sun zargi Babban Sakataren Ma’aikatar Kafa Hukumomi (Establishment) da gazawa wajen isar da koke-kokensu da buƙatunsu ga Gwamnan jihar.

Sun ce duk da irin shekarun da suka shafe suna yi wa jihar hidima, har yanzu suna fuskantar matsalolin rayuwa tare da iyalansu, ciki har da wasu daga cikinsu da ke da buƙata ta musamman da kuma masu fama da matsaloli masu tsanani.

Shugaban ƙungiyar ya kuma yi iƙirarin cewa Gwamna Kefas ya taɓa bayyana cewa an saki naira biliyan bakwai domin biyan buƙatun masu karɓar fansho, amma ya ce har yanzu ba su san abin da ya faru da kuɗin ko yadda aka yi amfani da su ba.

Masu zanga-zangar sun bukaci gwamnatin jihar ta binciki lamarin tare da daukar matakin gaggawa kan dukkan matsalolin da suka gabatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *