Wani fasinja ya rasu a cikin jirgin Kenya Airways yayin da yake kan hanyar sa ta zuwa Najeriya
Wani fasinja ya rasu a cikin jirgin Kenya Airways yayin da yake kan hanyar sa ta zuwa Najeriya
Wani fasinja ya rasu a cikin jirgin kamfanin Kenya Airways, yayin da jirgin ke kan hanyarsa daga Nairobi zuwa Legas, bayan ya daina motsi jim kaɗan kafin jirgin ya sauka a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas.
Kamfanin Kenya Airways ya ce lamarin ya faru ne jiya Talata da misalin ƙarfe 9:20 na dare agogon Najeriya, kimanin mintuna 20 kafin jirgin ya isa Legas.
A cewar kamfanin, ma’aikatan jirgin sun yi ƙoƙarin ba fasinjan agajin gaggawa tare da bin ƙa’idojin da aka tanada domin irin wannan yanayi.
Jirgin ya sauka a Legas da ƙarfe 9:41 na dare, inda jami’an lafiya suka shiga domin duba fasinjan, kafin daga bisani su tabbatar da cewa ya rasu.
Kenya Airways bai bayyana sunan mamacin ko musabbabin mutuwarsa ba, yana mai cewa yana aiki tare da iyalan mamacin da hukumomin Najeriya, da kuma hukumomin kula da harkokin zirga-zirgar jiragen sama.
