Babachir Lawal ya zargi Atiku da magudi a zaben fitar da gwani na ADC

0
Babachir Lawal ya zargi Atiku da magudi a zaben fitar da gwani na ADC

Babachir Lawal ya zargi Atiku da magudi a zaben fitar da gwani na ADC

Spread the love

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya sake zargin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da hannu wajen magudin zaben fidda gwani na jam’iyyar (ADC), wanda ya kai ga Atiku zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2027.

Lawal ya bayyana hakan ne a wata hira da Trust TV, inda ya ce zargin magudin na daga cikin dalilan da suka sa ya fice daga ADC.

Lawal ya ce tun farko ya goyi bayan Mohammed Hayatu-Deen, wanda ya bayyana a matsayin dan takarar da ya fi ganin ya dace da kujerar shugaban kasa.

Ya yi ikirarin cewa a jihar Adamawa, Hayatu-Deen ya samu kuri’u masu yawa, amma yayin tattara sakamakon, an sauya wasu daga cikin kuri’un da aka ce na Hayatu-Deen ne zuwa ga Atiku.

Ya ce ya yi kokarin kalubalantar abin da ya kira kura-kurai a tsarin zaben, amma hakan bai sauya sakamakon karshe ba.

Atiku dai an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani da kuri’u 1,846,370, yayin da Rotimi Amaechi ya samu 504,117, Hayatu-Deen kuma 177,120.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *