Amaechi ya gargadi Tinubu kan yunkurin magudin zaɓen 2027
Amaechi ya gargadi Tinubu kan yunkurin magudin zaɓen 2027
Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya gargadi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kada a yi magudin zaɓen 2027, yana mai cewa hakan na iya ƙara jefa Najeriya cikin matsala.
Amaechi ya bayyana cewa al’ummar Najeriya na fama da matsin tattalin arziki, inda ya ce mutane sun gaji kuma suna fama da yunwa sakamakon tsadar rayuwa da sauran ƙalubalen tattalin arziki.
Tsohon gwamnan Rivers ya kuma ce ba ya ƙin Tinubu a matsayinsa na mutum, amma ya jaddada muhimmancin gudanar da zaɓen 2027 cikin gaskiya da adalci, ba tare da karkatar da sakamakon zaɓe ba.
A cewarsa, ya kamata gwamnati ta fi mayar da hankali kan matsalolin da talakawa ke fuskanta, musamman tsadar rayuwa da farashin man fetur, yayin da ƙasar ke shirin shiga zaɓen 2027.
