’Yan sanda sun kara tabbatar da dokar haramta hawan dawakai da Durbar a Kano
’Yan sanda sun kara tabbatar da dokar haramta hawan dawakai da Durbar a Kano
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sake jaddada cewa har yanzu dokar hana dukkan nau’o’in Durbar da hawan dawakai ko a fadin jihar tana nan daram, tana kuma aiki.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a hedikwatar ’yan sanda ta Bompai, Kano, ranar Juma’a, 2 ga Oktoba, 2026.
Kwamishinan ya ce gwamnatin Jihar Kano ta dauki matakin ne bayan tuntubar hukumomin tsaro, da nufin kare zaman lafiya da lafiyar jama’a.
Ya bayyana cewa duk da dokar, an samu rahotannin wasu mutane na kokarin karya umarnin, yana mai cewa barazanar tsaron da ta sanya aka kafa dokar har yanzu tana nan.
Sai dai rundunar ’yan sandan ta ce duk wani mutum, kungiya ko hukuma da ke ganin ya zama dole ta gudanar da Durbar ko hawan dawakai a wuraren jama’a, dole ne ta sanar da rundunar ’yan sanda a rubuce akalla sa’o’i 72 kafin taron, ta hannun Ofishin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano.
Rundunar ta ce hakan zai ba jami’an tsaro damar yin tantancewar tsaro da kuma shirya yadda za a kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
CP Bakori ya yi kira ga al’ummar Kano da su mutunta umarnin tsaro tare da ba jami’an tsaro hadin kai wajen tabbatar da zaman lafiya.
Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa hukumomin tsaro a jihar sun hade kansu, kuma za su ci gaba da daukar matakan da suka dace wajen tabbatar da bin doka da kare lafiyar al’umma.
