Kalaman Jarumar Kannywood Rashida Mai Sa’a Kan Tsaron Najeriya Sun Jawo Cece-kuce
Kalaman Jarumar Kannywood Rashida Mai Sa'a Kan Tsaron Najeriya Sun Jawo Cece-kuce
Jarumar Kannywood Rashida Adamu Abdullahi Maisa’a ta ce duk da matsalolin tsaro da ake fuskanta a wasu sassan Najeriya, ƙasar na da ingantaccen tsaro fiye da yadda wasu ke bayyana a kafafen sada zumunta. Ta bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da ya bazu a yanar gizo.
Rashida ta ce mutane da dama suna ƙara girman matsalolin tsaro, alhali akwai wurare da dama a faɗin ƙasar da ke cikin kwanciyar hankali.
Ta kuma yi kira ga jama’a da su guji yaɗa bayanan da ka iya jefa mutane cikin fargaba ba tare da hujja ba.
Jarumar ta bayyana cewa duk da akwai ƙalubalen tsaro kamar yadda ake samu a sauran ƙasashe, hakan ba yana nufin Najeriya ba ta da tsaro gaba ɗaya ba. Ta buƙaci a riƙa kallon al’amuran tsaro cikin adalci da gaskiya.
Kalaman Rashida sun haifar da muhawara a kafafen sada zumunta, inda wasu suka goyi bayan ra’ayinta, yayin da wasu kuma suka ce har yanzu akwai buƙatar gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen magance matsalolin tsaro a sassan da abin ya fi kamari.
