Iyalan Laftanar Ademe sun koka kan yadda aka sanar da mutuwar dansu, sun nemi a girmama shi

0
Iyalan Laftanar Ademe sun koka kan yadda aka sanar da mutuwar dansu, sun nemi a girmama shi

Isaac Ademe

Spread the love

Iyalan marigayi Laftanar Felix Ademe Isaac, jami’in rundunar sojin Najeriya da ya rasa ransa yayin jagorantar aikin ceto ɗalibai da malamai da aka sace a ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo, sun bayyana alhini tare da zargin cewa hukumomin da abin ya shafa sun ɓoye musu cikakken bayani kan yadda ɗansu ya mutu.

Mahaifin marigayin, Master Warrant Officer (RSM mai ritaya) Isaac Alabura, ya ce har yanzu iyalan ba su farfaɗo daga jimamin rasuwar ɗan nasu ba.

Ya bayyana marigayin a matsayin babban abin alfaharin iyali da al’umma, yana mai cewa suna fatan ganin ya kai manyan mukamai a aikin soja kafin rasuwarsa ta katse wannan buri.

Alabura ya kuma nuna rashin jin daɗinsa kan shiru da rundunar sojin Najeriya da gwamnatin jihar Oyo suka yi kan lamarin.

Ya yabawa wasu manyan jami’an soja da suka taimaka wajen tabbatar da an kawo gawar marigayin Yola domin binne shi, duk da ƙoƙarin da aka yi na binne shi a jihar Oyo.

Shi ma ɗan uwan marigayin, Tidwawa Nelson Eweh, ya ce Najeriya ta yi babban rashi na hazikin jami’in soja mai kyakkyawan hali da jajircewa.

Iyalan sun buƙaci rundunar soji da gwamnatin jihar Oyo su girmama sadaukarwar marigayin tare da adana sunansa a tarihin ƙasa saboda irin hidimar da ya yi wa Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *