Najeriya ta kaddamar da shirin farfaɗo da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko
Farfesa Muhammad Ali Pate
Gwamnatin Najeriya ta fara aiwatar da shirin inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (PHC) a faɗin ƙasar nan domin samar da ingantattun ayyukan jinya ga al’umma, musamman masu nakasa, tsofaffi da sauran masu buƙatar kulawa ta musamman.
Ministan Lafiya da Jin Daɗin Al’umma, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya ce shirin zai bai wa jama’a damar samun ayyukan gyaran jiki da sauran muhimman kula na lafiya a cibiyoyin PHC, maimakon dogaro da manyan asibitoci kaɗai.
Gwamnatin ta bayyana cewa duk da Najeriya na da cibiyoyin PHC kusan 34,000, har yanzu ana fama da ƙarancin ƙwararrun ma’aikatan gyaran jiki da sauran masu ba da irin waɗannan ayyuka, lamarin da ake shirin magancewa ta hanyar ƙara horaswa da ɗaukar ma’aikata.
An ƙaddamar da shirin ne a jihar Bauchi, yayin da gwamnatin ta ce za a faɗaɗa shi zuwa sauran jihohin ƙasar domin ƙarfafa tsarin kiwon lafiya da rage wahalar da marasa lafiya ke sha wajen samun kulawar da suke buƙata.
