Sarkin Musulmi ya yi kira ga Arewacin Najeriya su haɗa kai domin murƙushe ƴan ta’adda
Sarkin Sarkin Musulmi, mai alfarma Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya buƙaci al’ummar Arewacin Najeriya su haɗa kai wajen yaƙi da ta’addanci da ƴan bindiga, yana mai cewa rashin tsaro ya zama babban ƙalubale da ke buƙatar haɗin kan kowa domin shawo kansa.
Ya bayyana cewa ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran ayyukan miyagu ba su da alaƙa da addinin Musulunci, yana mai kira da a daina jingina laifukan masu aikata ta’addanci da wata ƙabila ko addini.
Sarkin Musulmin ya jaddada cewa shugabannin gargajiya, na addini, hukumomin tsaro da kuma al’umma dole ne su yi aiki tare domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ta addabi yankin Arewa.
Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su kasance masu haɗin kai, bayar da sahihan bayanan sirri ga jami’an tsaro, tare da guje wa kalaman da za su haddasa rarrabuwar kawuna, yana mai cewa haɗin kai ne mafita wajen murƙushe ta’addanci da tabbatar da zaman lafiya.
