Zulum ya ba da umarnin rufe sansanin ƴan gudun hijira dake Bama saboda barazanar tsaro

0
Zulum ya ba da umarnin rufe sansanonin ƴan gudun hijira saboda barazanar tsaro

Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zullum

Spread the love

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ba da umarnin rufe sansanin ‘yan gudun hijira na Bama nan take, tare da sanar da cewa za a rufe na Gwoza cikin makonni biyu zuwa uku masu zuwa.

Zulum ya ce gwamnati ta ɗauki matakin ne bayan gano karuwar ayyukan ta’addanci da sauran laifuka a cikin sansanonin, inda ya yi zargin cewa wasu mayaƙan Boko Haram da ISWAP na kutsawa cikinsu.

Ya kuma bayyana cewa an gano wasu mutane da ba ‘yan gudun hijira ba suna fakewa a sansanonin domin karɓar tallafin ƙungiyoyin agaji, lamarin da ya sa gwamnati ta fara tantance mazauna sansanonin kafin mayar da su garuruwansu.

Gwamnan ya ce matakin na daga cikin shirin gwamnatin Borno na rufe dukkan sansanonin ‘yan gudun hijira tare da mayar da waɗanda abin ya shafa zuwa yankunansu cikin tsaro da mutunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *