NUC ta amince da kafa sabuwar jami’a a Taraba ta fannin Noma da Kimiyya da Sauyin Yanayi
NUC ta amince da kafa sabuwar jami'ar Taraba ta fannin Noma, Kimiyya da Sauyin Yanayi
Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta amince a hukumance da kafa Jami’ar Taraba ta Noma Mai Zafi, Kimiyya, Fasaha da Ayyukan Sauyin Yanayi (TSU-TASCA) da ke Gembu, inda ta ayyana ta a matsayin sabuwar jami’ar gwamnati a Najeriya.
Sakataren Zartarwa na NUC ya bayyana cewa wannan amincewa wata babbar nasara ce ga bangaren ilimi, yana mai jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da bai wa jami’ar cikakken goyon baya domin tabbatar da bin ka’idojin ingancin ilimi da NUC ta tanada.
A jawabinsa yayin bikin amincewar, Gwamnan Jihar Taraba, Dakta Agbu Kefas, ya ce an kafa jami’ar ne domin gina cibiyar ilimi ta duniya wadda za ta mayar da hankali kan noma, kirkire-kirkire a fannin kimiyya, kare muhalli da kuma magance kalubalen sauyin yanayi.
Ana sa ran sabuwar jami’ar za ta taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa jarin ɗan Adam, ƙarfafa bincike da kirkire-kirkire, tare da faɗaɗa damar samun ingantaccen ilimin jami’a da kuma tallafawa ci gaba mai ɗorewa a Najeriya.
