Radda ya sha alwashin kawo karshen matsalar ruwa a Katsina
Dikko Radda Umaru
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sha alwashin kawo ƙarshen matsalar ƙarancin ruwa da ta daɗe tana addabar al’ummar jihar, yana mai cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari a ayyukan samar da tsaftataccen ruwa.
Radda ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da aikin samar da ruwa na Tsagero, inda ya ce samun ruwa mai tsafta haƙƙi ne na kowa kuma muhimmin ginshiƙi ne na lafiya da ci gaban tattalin arziki.
Ya ce gwamnati ta kammala da dama daga cikin ayyukan samar da ruwa da aka fara, yayin da ake ci gaba da wasu domin faɗaɗa isar da ruwa zuwa ƙarin al’ummomi a faɗin jihar.
Gwamnan ya tabbatar wa al’ummar Katsina cewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai an samar da isasshen ruwa mai tsafta ga mazauna birane da karkara baki ɗaya.
