Osoba ya yi zargin ana shirya takaran Peter Obi, Jonathan da Makinde don rage kuri’un Tinubu a Kudu

0
Olusegun Osoba

Olusegun Osoba

Spread the love

Tsohon gwamnan jihar Ogun, Olusegun Osoba ya bayyana cewa akwai wasu shirye-shiryen siyasa da ake yi domin raba kuri’un Kudancin Najeriya da ake ganin za su iya komawa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Osoba ya ce ana kokarin fito da fitattun ‘yan siyasa irin su Peter Obi, Goodluck Jonathan da kuma Seyi Makinde domin tarwatsa karfin kuri’un yankin Kudu.

Rahotanni sun nuna cewa Osoba ya bayyana damuwarsa kan yadda yawaitar ‘yan takarar Kudu zai iya bai wa yankin Arewa damar samun rinjaye idan ba a samu hadin kai ba.

Ya ce idan manyan ‘yan siyasa daga Kudu suka tsaya takara daban-daban, hakan na iya rage damar kayar da jam’iyya mai mulki a babban zaben 2027.

A gefe guda kuma, wasu masu sharhi kan siyasa sun ce shiga takarar da Seyi Makinde ke yi ya kara rikitar da lissafin siyasar Kudu, musamman ganin cewa akwai yiwuwar Peter Obi ma ya sake neman shugabanci.

Sun ce rashin dunkulewar ‘yan adawa na iya zama babban kalubale ga kokarin kifar da gwamnatin APC a 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *