Gwamnatin tarayya ta ayyana Laraba da Alhamis hutun Sallah

0
Gwamnatin Tarayya Ta Ayana Laraba Da Alhamis Hutun Sallah

Gwamnatin Tarayya Ta Ayana Laraba Da Alhamis Hutun Sallah

Spread the love

Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranakun Laraba 27 ga watan Mayu da Alhamis 28 ga watan Mayu, 2026 a matsayin ranakun hutun gwamnati domin bikin Eid-ul-Adha, wato Babbar Sallah.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan ta bakin Sakatariyar din-din-din ta ma’aikatar, Magdalene Ajani.

A cikin sanarwar, gwamnatin ta taya al’ummar Musulmi murnar wannan babban biki mai muhimmanci a addinin Musulunci, tare da jaddada cewa Sallah lokaci ne na sadaukarwa, biyayya ga Allah da kuma taimakon juna.

Haka kuma gwamnati ta bukaci ‘yan Najeriya su yi amfani da lokacin wajen addu’ar zaman lafiya, hadin kai da ci gaban kasa.

Ministan ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da rungumar soyayya, hakuri da zaman lafiya kamar yadda addinin Musulunci ya koyar.

Ya ce gwamnatin tarayya na ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai tsakanin ‘yan Najeriya ba tare da nuna bambanci ba.

Rahotanni sun nuna cewa hutun na bana ya zo daidai da bukukuwan Babbar Sallah da ake sa ran Musulmai za su gudanar a fadin duniya, yayin da hukumomi suka bukaci jama’a su gudanar da bukukuwansu cikin lumana da bin doka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *