PDP ta amince da Maurice Vunobolki a matsayin dan takarar Gwamnan Adamawa
Chief Maurice Vunobolki
Jam’iyyar PDP ta tabbatar da Chief Maurice Vunobolki a matsayin dan takararta na kujerar gwamnan Jihar Adamawa gabanin zaben shekarar 2027.
Jam’iyyar ta bayyana cewa Vunobolki ne kadai ya bayyana aniyarsa ta neman tikitin takarar gwamna a karkashin PDP, lamarin da ya sa aka tabbatar da shi ba tare da wata hamayya ba.
Rahotanni sun nuna cewa matakin na PDP ya zo ne bayan Vunobolki ya fice daga jam’iyyar APC tare da komawa PDP, inda ya zargi tsohuwar jam’iyyarsa da rashin adalci da kuma yunkurin kakaba ‘yan takara kafin zaben fidda gwani.
Bayan dawowarsa PDP, magoya bayansa daga sassa daban-daban na Adamawa suka fara nuna goyon baya ga takararsa.
A cikin sanarwar da jam’iyyar ta fitar, PDP ta bayyana Vunobolki a matsayin gogaggen dan siyasa kuma wanda ke da hangen nesa wajen kawo ci gaba da hadin kai a jihar Adamawa.
Jam’iyyar ta kuma bukaci magoya bayanta su hada kai domin tabbatar da nasara a babban zaben 2027.
Tabbatar da Vunobolki a matsayin dan takarar gwamna ya fara daukar hankalin masu sharhi kan siyasa, musamman yadda ake ganin fafatawar siyasar Adamawa za ta kara zafi a shekarar 2027.
