Rikici ya kaure a APC kan takarar Mustapha Salihu na sanatan Adamawa ta tsakiya – Isma’il
Comrade Mustafa Salihu
Fitowar Mustapha Salihu a matsayin ɗan takarar Sanatan Adamawa ta tsakiya na jam’iyyar APC ta sake tayar da muhawara kan yadda jam’iyyun siyasa ke sauya wa ‘yan takara gurbi bayan kammala zaɓukan fidda gwani.
Wani marubuci, Mohammed Ismail, ya bayyana cewa lamarin na ƙara nuna matsalolin da suka dabaibaye tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya, musamman yadda ake zargin wasu jiga-jigan siyasa da amfani da ƙarfin iko wajen sauya sakamakon zaɓen cikin gida.
Rahoton ya nuna cewa tun farko Mustapha Salihu bai da wata alaƙa da takarar Sanatan Adamawa ta Tsakiya, domin dukkan shirye-shiryensa sun karkata ne kan neman tikitin takarar gwamnan jihar Adamawa a ƙarƙashin APC.
Ya sayi fom ɗin takara, ya kafa ƙungiyoyin yaƙin neman zaɓe a faɗin ƙananan hukumomi 21 na jihar tare da gudanar da gangamin neman goyon baya domin cimma burinsa na zama gwamna.
Sai dai bayan kammala takarar gwamna ne kwatsam aka bayyana shi a matsayin ɗan takarar Sanata, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce daga masu sharhi kan siyasa.
Marubucin ya danganta hakan da irin rikice-rikicen siyasar da suka faru a baya, ciki har da batun tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan da kuma Shugaban Majalisar Dattawa na yanzu, Godswill Akpabio, waɗanda suka fuskanci zarge-zargen sauya takara bayan wasu zaɓukan fidda gwani.
A cewar marubucin, abin da ke gaban al’umma yanzu ba wai batun sayen fom ko miƙa suna ga INEC kaɗai ba ne, illa tambayar ko an gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani cikin gaskiya da adalci.
Ya gargadi cewa idan aka ci gaba da barin irin waɗannan sauye-sauye ba tare da bin ƙa’ida ba, hakan na iya raunana dimokuraɗiyya tare da mayar da zaɓe tamkar wata hanya ta biyan buƙatun masu iko maimakon muradin jama’a.
