Tsohon shugaban NIRSAL, Aliyu Abbati ya bayyana niyyar tsayawa takarar Sanata a Adamawa ta tsakiya
Tsohon shugaban NIRSAL, Aliyu Abbati ya bayyana niyyar tsayawa takarar Sanata a Adamawa ta tsakiya
Tsohon Manajan Darakta kuma Babban Jami’in NIRSAL, Alhaji Aliyu Abbati Abdulhameed, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Sanata mai wakiltar Adamawa ta Tsakiya a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2027.
Ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a Yola, inda ya ce burinsa shi ne samar da ingantacciyar wakilci ga al’umma a Majalisar Dokoki ta Ƙasa.
Abbatti ya bayyana cewa ba zai je Abuja domin zama kawai ba, sai dai domin yin aiki tukuru wajen ƙirƙirar dokoki, kare muradun al’umma, da jawo ayyukan ci gaba zuwa jihar Adamawa.
Ya buƙaci al’ummar mazabar su mara masa baya domin samun nasara a zaɓe, yana mai cewa wakilci nagari shi ne ginshiƙin ci gaban al’umma.
Ya kuma bayyana cewa yankin Adamawa ta Tsakiya na da albarkatu da dama kamar ƙasa mai kyau, amma duk da haka yana fuskantar matsaloli irin su ambaliya, rashin aikin yi da ƙarancin ababen more rayuwa.
Ya yi alƙawarin amfani da ƙwarewarsa musamman a fannin noma domin kawo sauyi da inganta rayuwar al’umma.
Tsohon shugaban na NIRSAL ya jaddada muhimmancin dogaro da kai ga al’umma, musamman mata da matasa, tare da alƙawarin yaƙi da talauci, inganta noma da kuma magance rikicin manoma da makiyaya.
Haka kuma ya bayyana shirinsa na yin aiki tare da Ma’aikatar Kiwo ta Tarayya domin samar da hanyoyin rage ambaliya da inganta rayuwar karkara.
Abbatti ya nuna gamsuwa da tsarin jam’iyyar APC wajen zaɓen ‘yan takara, yana mai cewa zai mutunta duk wata matsaya da jam’iyyar ta ɗauka.
Ya kuma yabawa gwamnatin tarayya ƙarƙashin Bola Ahmed Tinubu da kuma Gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, kan kokarinsu na inganta tsaro da ci gaban ƙasa.
